Sanata mai wakiltan Katsina ta Kudu da dan majalisan da ke wakiltan Kananan hukumomin Bakori da Danja a majalisar wakilai sun sha da kyar a taron jam’iyyar APC da akayi a garin Funtua.
Kamfanin dillancin labarai ta rahoto cewa jami’an ‘yan sanda ne suka kawo musu dauki da ya hada da tawagar gwamnan jihar Aminu Bello Masari.
Sun sha ruwan duwatsu da takalma a harin inda sai da akayi amfani da barkonun tsohuwa kafin aka samu shawo kan matasan.
Gwamna Masari da sanata Abu Ibrahim suna halartar taron karban wasu ‘Ya’yan jam’iyyun PDP, APGA da PDM ne da suke canza sheka zuwa jam’iyyar APC.
Ba’a dade da fara taron ba kwatsam sai matasa suka fara ihun “Ba ma son Abu Ibrahim ba ma so” sai suka fara jefar bakin da duwatsu da takalma.
Dan majalisa Amiru Tukur ya samu raunuka a harin inda wasu da suka nemi kare Abu Ibrahim suma suka sami nasu rabon ruwan duwatsun.
Sama da mutane 5000 ne suka canza sheka zuwa jam’iyar APC a taron.