An saki Nnamdi Kanu

0

Bayan gindaya masa sharuddan da sai ya cika kafin a sake, yau Juma’a Jagoran kafa jamhuriyar Biafara Nnamdi Kanu ya fice daga kurkukun Kuje inda yake tsare.

Ga sharuddan da Nnamdi Kanu ya ci ka.

1 – Kada ya sake ya tsaya ko ya zauna tare da gungun mutanen da suka haura 10.

2 – Kada ya sake ya yi hira da ‘yan jarida.

3 – Kada ya tara gangamin jama’a.

4 – Ba za a karbi belin saba, har sai ya kawo mutane uku sun tsaya masa tare da ajiye kudi naira milyan 100 kowanensu.

5 – Daya daga cikin masu karbar belin ya kasance wani babban mutum ne kuma Inyamiri, musamman Sanata.

6 – Mai karbar belin na biyu ya kasance Bayahude ne, tunda Nnamdi Kanu adddinin Yahudawa ya ke bi.

7 – Mai karbar beli na uku ya kasance babban mutum ne mazaunin Abuja, wanda ya mallaki gida ko fili a Abuja.

8 – Tilas Nnamdi Kanu ya bai wa kotu ajiyar Pasport din sa na fita kasasshen waje.

9 – Shi ma passport din sa na kasar Birtaniya ana so ya bayar wa kotun ajiyar sa.

10 – Ana so duk wata ya kai wa kotu bayanin irin saukin da ya ke samu da kuma irin kulawar da likitoci suka yi masa.

Share.

game da Author