Shugabannin gidauniyoyin Dangote da Bill da Melinda Gates sun sanar da cewa gidauniyoyin su sun dukufa domin ganin an raba kasashen yankin tekun Chadi daga annobar cutar shan inna ta hanyar samar da gudunmawar alluran rigakafi ga kasahen.
Sun fadi hakan ne a wata sako ta musamman da suka bayar a taron tunawa da yin rigakafi na duniya wanda aka fara tun a ranar 24 gawatan Afirilu.
Sun shaida cewa za su dauki ma’aikatan bada alluran rigakafi daya kai 138,000 wanda za su yi aiki a kasashen Najeriya, Niger, Chad, Cameroon da jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
Sun kuma jinjina wa kasa Najeriya akan yadda suka sami nasarar kawar da cutar kashi 95 bisa 100 duk da cewa har yanzu ana samun karancin ma’aikata da suke shiga jihar Barno saboda aiyukkan Boko Haram a jihar.
Bayan haka shugabanin gidauniyoyin su ce sun hada hannu da wasu gwamnatin jihohin kasa Najeriya domin taimakawa fannin kiwon lafiyar kasar.
Sun ce sun hada hannu da gwamnatin jihar Kano domin bunkasar da finnin kiwon lafiya musamman wajen ganin cewa yara da mata masu dauke da juna biyu sun sami rigakafin cutar dajin dake kama huhu, cutar zazzabin cizon sauro cutar da ake kamawa idan an sami rauni da karfe wato Tetanus da kuma samar da kula wanda zai taimaka wa yara kanana su girma yadda ya kamata.
Sun kuma ce sun hada hannu da wata kungiya mai zaman kanta domin kawar da cutar maleriya da kuma samar da hanyoyin da zai rage talauci da kuma kawo ci gaban da kasan ke bukata.