Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya ce gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya rusa gidan Inuwa AbdulKadir ne dake Kaduna saboda adawar siyasa kawai amma ba don wani abu ba.
Ranar Larabar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kaduna ta rusa gidan mataimakin shugaban Jam’iyyar APC na shiyar Arewa Maso Yamma dake kan titin Yakubu Avenue, Kaduna.
Gidan jaridar Daily Trust ta ba da rahoton cewa Sanata Sani ya fadi hakan ne da ya kai ziyarar yi wa Inuwa jaje akan abin da gwamnatin Kaduna tayi masa.
” Abinda akayi maka siyasa ce kawai. Kuma anyi maka hakanne domin tsayawa da kayi tsayin daka don ganin kowa ya bi dokar jam’iyyar kamar yadda take.
” Ina so in sanar maka cewa anyi maka wannan cin mutuncin ne saboda ni. Amma yanzu kowa ya sani cewa a dalilin kokarin ka ne na shugaban Jam’iyyar a shiyar Arewa Maso Yamma ka ga an samu daidaituwa tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar ya sa hakan ya faru.
“Abin kunya ne ace wai wadanda suke kiran kansu yan siyasa kuma ace ba za su iya jure ma adawa ba.
Daga karshe Inuwa AbdulKadir ya ce ba zai ce komai akai ba domin maganar na kotu a yanzu hakan.
“Kuma duk da haka ina so in sanar wa ‘yan Najeriya cewa hakan ba zai sa in kauce daga aikin da na ke yi wa jam’iyya ba a matsayina na shugaban Jam’iyyar a shiyar Arewa Maso Yamma.” Inji Inuwa AbdulKadir.
Discussion about this post