Rikicin da ya tirnike cikin uwar jam’iyyar PDP ya kara murdewa, inda har mai bai wa shugaban jam’iyyar shawara a harkokin yada labarai, Inuwa Bwala ya sauka daga aikin sa.
Bwala ne da kansa ya bayyana haka a jiya Lahadin da ta gabata.
A cikin wani jawabi da ya raba wa kafofin yada labarai, Bwala ya bayyana cewa rikicin jam’iyyar ya na shafar irin yanayin aikin sa, dalili kenan ya ga tilas ya jefar da kwallon magwaro, ya huta da kuda.
Ya kara da cewa sannan kuma akwai dalili na kashin kansa ya ga cewa akwai bukatar ya ajiye aikin domin ya maida hankali wajen kula da lafiyar sa.
“Ina bai wa ‘yan Najeriya hakuri, musammam shugabannin siyasar mu da kuma abokai na ‘yan jarida, wadanda na sha faman gaganiya da su wajen kokarin kare muradin Sanata Ali Modu Sheriff a lokacin da na ke kakakin yada labaran sa.
Sannan kuma ina yi masa fatan alheri.”