Rikicin PDP: Jonathan ya roki kowa ya maida wuka a cikin kube

0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, ya roki bangarori biyu na shuagabancin PDP da su maida wukaken su a cikin kube, a daina husuma domin su ciyar da jam’iyyarsu gaba.

Jonathan ya fadi hakanne a taron jam’iyyar wanda bangarorin biyu suka halarta.

“Lokaci fa ya yi da za mu daina nuna gaba da sauran bambance-bambance, mu tashi mu sadaukar da kanmu ga jam’iyyar mu da kuma kasa baki daya.” Haka Jonathan ya bayyana a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron, jiya a dakin taro na Yar’Adua Center, Abuja.

Wannan jawabi ya zo ne a daidai lokacin da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa ke ta kara ruruwa a cikin jam’iyyar PDP, wacce a yanzu ita ce jam’iyya mafi girma daga cikin jam’iyyun adawa.

“Ina kara sanar da mu cewa, yau ba rana ba ce da za mu zauna mu na dora laifi ko zargin wsunmu ba. Duk wasu munanan kalamai da zargin juna ko dora wa juna laifi, babu wanda a baya ba mu yi ba a kafafen yada labarai.. Don haka ya kamata mu sani cewa jam’iyya fa ita ce karfin kowa, domin duk karfin ka idan ba ka da jam’iyya, to ba ka da wani karfi.”

A taron gangamin jam’iyyar sau biyu da ta yi a shekarar da ta gabata, duk Sanata Ahmed Makarfi ne aka zaba a matsayin shugaba, abin da Sanata Ali Modu Sheriff ya kekesa kasa ya ce bai yarda ba, kuma ya garzaya kotu.
Dangane da haka ne kotun daukaka kara ta bayyana shi a matsayin shugaba, duk da dai har yanzu wannan rikicin shari’a a a gaban kotun kolo ta kasa.

Ficewar Ali Modu Sheriff daga zauren taro

Ana cikin taro ne a ranar Alhamis da ta gabata, sai Sanata Ali Modu Sheriff ya fice daga zauren taron, inda ya ce ai shi ne ya kamata ya bude taron a matsayin sa na halastaccen shugaban jam’iyya. Hakan ne ya sa Mista Olarenwaju ya ce ficewar Ali Sheriff daga taron ya nuna cewa har yanzu akwai sauran jan-aikin dinke Baraka a cikin jam’iyyar PDP.

“Na mutunta ‘yan jam’iyya na zo wannan taro, amma babban rashin adalci ne a ce ba a ba ni ko damar da zan yi wani jawabi ba.” Inji Sheriff.

Jonathan ya ce “PDP ba ta fadi zabe ba don wai ba ta gudanar da ayyuka ba. Duk duniya jam’iyya mai mulki na faduwa zabe, sai kawai saboda jama’ar da suka zabe su sun yanke shawarar sake ba da mulki ga wata jam’iyya domin su dandani wani salon shugabanci na daban. Ya ce tabbas PDP za ta dawo da karfin ta na jam’iyya mafi karfi a Afrika.”

Share.

game da Author