Gwamnatin Najeriya na shirin dakatar da wasu ayyukan da ta keyi a kasashen waje guda 119.
Ministan aiyukkan kasahen waje Geoffrey Onyeama ne ya fadi hakan da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai a Abuja.
Ya ce dakatar da wasu aiyuka da kasa Najeriya ke ciki kuma ta ke gudanar wa a wasu kasashe zai sa a sami ragi wajen dimbin kudaden da ake kashewa na gaira babu dalili.
Onyeama ya kuma kara da cewa wannan shiri na daya daga cikin shiriye-shiryen gyara kasa Najeriya da kuma rage almubazzaranci da akeyi da kudaden kasar da gwamnatin buhari ta sa a gaba.
Ko da yake minister Onyeama bai fadi wasu ayyuka bane gwamnatin za ta dakatar a kasashen wajen yace yin hakan yana da dan karan tsada.
“ Duk da mun sani cewa dakatar da aiyuka da ya shafi irin wannan ya na da tsada, amma ribar da za’a samu bayan haka na da amfani matuka.