Dan majalisar wakilai Abdulmumini Jibrin Ya roki jama’ar kananan hukumomin da ya ke wakilta da shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan maganganun da yayi cewa “ya kamata Buhari ya sauka daga kujeran shugabanci Najeriya.”
Abdulmumini ya ce duk da cewa ba’a fahimce sa bane domin ba abin da ake ta yadawa bane yake nufi amma dai tun da daga bakinsa ta fito, yayi nadama sannna ya na rokon ‘ya’yan jam’iyyar na mazabunsa da uwar jam’iyyyar ta kasa da shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari da su ya fe masa.
Bayan haka kuma ya jagoranci saukar Alkur’ani mai girma da ya sa ayi domin samun lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari a babbar masallacin Kofa da ke Kano.
Bayan an kammala karatun, an yanka bijimin sa domin yin sadaka da niyyar Allah ya amsa Addu’o’in da akayi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari da samun nasara a gwamnatin sa.