Na ka Ne, Ba nawa Bane : Wai shin dalolin wa ye aka gano a Legas?

0

Mutanen Najeriya sunanan sun kasa kunnuwa domin jin shin wanene ainihn mamallakin dalolin da hukumar EFCC ta kwato a jihar Legas.

Hukumar EFCC ta kwato wasu makudan daloli da aka boye a wani gida a jihar Legas.

Kudaden da aka kwato sun kai naira Najeriya Biliyan 13.

Saboda kulle-kullen da ke tattare da wannan kudade da aka gano, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa wata kwamiti da mataimakin sa Yemi Osinbajo zai shugabanta domin gudanar da bincike da gano ainihin mamallakin kudaden da kuma daga ina suka fito.

Shugaban hukumar lekan asiri wato NIA Ayo Oke ya sanar ma wannan gidan Jarida PREMIUM TIMES cewa wannan kudi na hukumarsa ne kuma sun ajiyesu a wannan gida domin wani aiki da za suyi da kudaden.

Duk da cewa tun a wancan lokacin da jami’an hukumar EFCC ke kokarin kwaso kudin daga inda aka boye su wato a gidan Ikoyi, Legas Ayo Oke ya ce ya kira shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu domin ya sanar dashi cewa ya dakatar da ma’aikatansa amma yayi burus dashi.

Ayo Oke ya ki ya sanar da mu ko kudin na me nene.

Ana cikin wannan hayagagar ne kuma sai gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike yace ai kudaden na jihar Ribas ne da tsohon gwamnan jihar Rotimi Amaechi ya wawura lokacin ya na gwamna. Bayan haka Amaechi wanda shine ministan sufurin kasa ya musanta hakan inda yayi barazanar maka gwamnatin jihar Ribas din a kotu cewa sun yi masa kazafi ne.

Ganin haka ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin a mai da kudaden babban bankin Kasa har sai an gudanar da bincike akansu.

Yanzu dai a halin da ake ciki allura na neman ya hako garma domin har tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai amsa tambayoyi akai.

Ayo Oke ya sanar da cewa an fidda kudaden ne tun a zamanin tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan amma ba’ayi amfani da su ba. A dalilin haka zai sa kila kwamitin su neme shi domin ya basu bayanai akan abin da ya sani game kudaden.

Shima gwamnan babban bankin Kasa Emiefele, zai fuskanci kwamitin Osinbajo, domin shine gwamnan babban bankin kasa a lokacin da aka fitar da dalolin daga bankin.

Oladimeji, wanda shine tsohon shugaban hukumar NIA zai masa tambayoyi domin kuwa Ayo na yanzu y ace tin a lokacinsa ne aka bada kudin.

Ko daya ke ba a Ambato sunan sa ba, tsohon gwamnan jihar Bauchi Adamu Mu’azu ne ya fara mallakar gidan da aka yi ajiyan wadannan daloli in da ya ce bayan ya gina gidan ya siyar da gidan da dadewa domin ya biya bashin bankin da yaci ya gina gidan.

Yanzu dai dabara ya rage wa mai shiga rijiya, ko su fito su fadi gaskiya ko kuma kwamitin Osinbajo ya tona wa duk mai hannu a ciki asiri.

Karanta labarin a shafin mu na turanci a nan: EXCLUSIVE: Jonathan, Emefiele, Magu, others to be questioned by presidential panel probing N13 billion Ikoyi money

Share.

game da Author