Mutane biyar sun rasa rayukansu a harin Bam a jihar Barno

0

Mutane biyar ne suka rasa rayukansu sannan wasu 11 suka sami raunuka a wata harin bam da ‘yan kunar bakin wake suka kai a karamar hukumar Muna, jihar Barno.

Unguwannin da harin ya shafa sun hada da Muna Usmanti, Muna Garage, da Muna Ethopia.

‘Yan kunar bakin wake su hudu duka ne suka rasa rayukansu a harin inda daya daga cikin ‘yan banga ya rasa ransa shima.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Barno Ibrahim Abdulkadir ya sshaida wa manema labarai cewa humarsa ta isa wajen da wannan mummunar abu domin bada agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.

“ Mun kai duka wadanda suka sami raunuka asibiti sanna zuwa yanzu an kwashe gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu zuwa inda ake ajiye gawawwaki a asibiti.”

Share.

game da Author

Comments are closed.