Kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines ta ce jiragen ta sun yi jigilan matafiya sama da 4,500 tun da ta fara aiki a tashar jiragen saman Kaduna.
Manajan kula da harkar kasuwanci na kamfanin Firiehiwot Mekonnen, ta ce a tsawon wadannan kwanaki jiragen Ethiopian Airlines sun yi sawu 28 na jigilan matafiya daga filin jiragin saman.
Mekonnen ta kara da cewa kamfanin na taya gwamnati murna ganin yadda aka ci karfin aikin da akeyi a filin jiragen saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
‘’Ba mu ga hanyar jirgin saman da ake gyarawa ba amma bisa ga labaran da muke samu akan gyaran gwamnati na kokarin ganin an bude filin jirgin kamar yadda ta yi alkawari.
A wata hiran da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta yi da ministan jiragen sama Hadi Sirika yace daga ranar 30 ga watan Maris jiragen sama 50 sun tashi zuwa kasashen waje inda suka kwashi fasinjoji 4,000 daga Kaduna.
Kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines ce kawai cikin jerin jiragen saman da suke jigia a kasa Najeriya suke tashi da ga Kaduna zuwa kasashen waje.
Jiragen sama na Arik da Medview suna jigilan fasinjoji zuwa kasahen waje da ga Kaduna inda a ranar 29 ga watan Maris Arik ta yi sawu 11 zuwa kasashen waje dauke da fasinjoji 165.
Discussion about this post