Mun fara ganin alfanun tafiye-tafiyen Buhari kasashen waje

0

Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama, ya bayyana cewa tafiye-tafiyen da Shugaba Muhammadu Buhari ya rika yi zuwa kasashen waje sun fara haifar da ‘ya’ya masu idanu.

Onyeama ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai wa ofishin Kamfanin Dillanci Labarai, NAN a Abuja, inda ya ce an fara samun nasara a fannonin tsaro da kuma tattalin arzikin kasa.

Ya ce ziyarce-ziyarcen da Buhari ya yi sun fara karkato hankulan masu sha’awar zuba jarin kasuwanci a Nijeriya, wanda hakan zai haifar da samun zuba jari kai tsaue daga kasashen waje.

Ministan ya ci gaba da cewa ziyarce-ziyarcen sun kara fito da sabuwar alkiblar Najeriya a idon duniya, wadanda kafin hawan wannan gwamnati ba su yi amannar yin kasadar zuba jari a Nijeriya ba.

“A baya mun sha fama da masu wawurar dukiyar al’umma ba ji ba gani, sannan kuma muka afka cikin halin karyewar kasuwar danyen man fetur. Don haka fitar da Buhari ya rika yi sun hada da samun kasashen da za su yi amanna da gwamnatin sa su yi hulda tare.”

“To sai ya fara gano matsalar mu ta farko ita ce matsalar tsaro, wacce nan da nan kuma ya fara warware ta. Idan za ku iya tunawa kafin wannan gwamnatin ai kasashe da dama sun daina sayar wa Nijeriya makamai, kuma suka daina yin kowace irin hulda ta sojoji da mu.”

Share.

game da Author