A cikin wannan mako ne shugaban kasa Nuhammadu Buhari ya Kaddamar da shirin farfado da tattalin arzikin Kasa.
Gidan Jaridar PREMIUM TIMES ta yi muku fashin baki akan kudirorin sannan ta kawo muku muhimman abubuwa 21 da kasa za ta amfana da su.
1 – Wannan shiri ya na kunshe ne da wasu muhimman tsare-tsare uku da ake son aiwatarwa: Wato dawo da martarbar tattalin arziki, zuba jari da kuma gina tattalin arziki wanda zai yi gogayya da tattalin arzikin kasashen waje.
2 – Ana hankoron inganta ababen da kasar nan ke samarwa da kanta zuwa kashi 2.19 a cikin 2017, yayin da ake kyautata yakinin zai karu zuwa kashi 7.0 nan da shekarar 2020.
3 – An saisaita wannan tsari ne da nufin rage matsin fatara da talauci da hauhawar farashi yadda ba zai rika haura kashi 9 bisa 100 ba, nan da shekarar 2020. Sannan kuma za a kara samun kudin shiga ga gwamnatin tarayya, daga naira tiriliyan 2.7 a cikin 2016 zuwa naira tiriliyan 4.7 ya zuwa shekarar 2020.
4 – Shirin zai fi maida hankali ne wajen samar da dawwamammen ci gaban al’umma na zahiri a cikin 2017 ta hanyar saisaita shirin inganta tattalin arziki a tsari mai matsakaicin zango tsakanin 2017 zuwa 2020.
5 – Shirin zai maida hankali wajen habbaka kananan masana’antu ta yadda za su zauna da gindin su, inganta tattalin arziki tare kuma da yanayin mai kyau domin gudanar da kasuwanci da inganta tsaro.
6 – An gina wannan shiri ne a kan tsarin tattalin arziki mai gajeren zango, SIP, daga cikin kasafin kudi na 2016, da aka fi sani da Kasafin Jaddada Canji a matsayin tushen kaiwa gacin shirinn tattalin arziki na 2017 zuwa 2020.
7 – Wannan shiri wani makami ne mai kaifi uku, wato dakile wawurar dukiya, tsaro da kuma sake gina tattalin arziki.
8 – Zai tafiya ne kafada-da-kafada da shirin muradin gina tattalin arziki na SDGs, domin zai shawo kan matsalar tattalin arziki, zamantakewa da inganta muhalli.
9 – Wannan tsari ya sha bamban da irin wasu shirye-shirye da aka fito da su a gwamnatocin baya. Domin a yanzu akwai kyakkyawan kudirin tabbatar da samun nasarar shirin daga gwamnati.
10 – Shirin na da wani sashen da ke kula da shi daga fadar shugaban kasa, domin tabbatar da samun nasara.
11 – An tsara yadda za a kara samun yawan danyen man fetur din da ake hakowa zuwa ganga milyan 2,5 nan da 2020.
12 – Za a saida wasu masana’antu ko hannayen jarin gwamnati ga ‘yan kasuwa, za a farfado da matatun man fetur domin ganin an daina shigo da kashi 60 cikin 100 na fetur daga kasashen waje.
13 – An gina wannan tsari ne a kan tubalin Shirin Farfado Da Masana’antu Na Kasa da kuma shirin inganta kayayyakin alfanu na kasar nan.
14 – Shirin zai yi tafiya tare da hadin kan gwamnatin jihohi da kananan hukumomi domin domin tabbatar da samun nasara a kasa baki daya.
15 – Zai kara jaddada kwazon gwamanti da ‘yan kasuwa wajen gina kyakkyawan ci gaban tattalin arziki, samar da abinci, hasken lantarki da inganta tsaro.
16 – Zai maida hankali wajen magance matsalolin da suka dabaibaye shirin inganta tattalin arziki ta hanyar karfafa masana’antu masu zaman kansu wajen sake farfado da tattalin arziki.
17 – Shirin na da wasu manyan fulogan da za su zaburad da shi a lokaci guda: saisaita kananan masana’antu, samun nasarar inganta abinci da harkokin noma a kasa, tabbatar da wadatuwar makamashi a fannin hasken lantarki da danyen mai, inganta harkokin sufuri, da kuma inganta kananan masana’antu da ‘yan kasuwa.
18 – Shiri ne domin kai gacin inganta tattalin arziki mai na gajeren zango da kuma na dogon zango.
Shirin ya hade ayyukan kasafin kudi da na tsare-tsare a ma’aikata guda, domin samar da kyakkyawar alaka tsakanin kasafin kowace shekara da kuma tsarin tattalin arziki.
19 – Shirin zai bada himma wajen karin samun kudaden shiga daga naira bilyan 700 cikin 2016 zuwa naira tiriliyan 1.3 a cikin 2017. Sai kuma naira tiriliyan 1.45 a kowace shekara daga 2020.
20 – Shirin ya dauki damarar inganta kudaden shiga a fannin man fetur daga hako ganga milyan 1.4 a kowace rana a 2016 zuwa hako ganga milyan 2.2 a cikin 2017 da kuma ganga milyan 2.5 a 2020.
21 – Shirin zai rage hanyoyin kashe kudade a gwamnati har kusan naira bilyan 50 a kowace shekara, wato kashi 25 bisa 100.