Wata mata mai suna Fatima ta maka mijinta a kotu saboda guduwa da yake da zaran ya tabbatar ta dauki ciki.
Fatima ta ce mijinta ya bukace ta da ta zubar da cikinta na biyu amma da taki sai ya tattara nasa-ina-sa ya gudu daga gidan da suke zama.
Ta roki kotu da ta raba wannan aure nasu ko dan saboda ‘ya’yan da suka haifa da mijin na ta.
Da yake bada bayanan sa akan wannan zargi mijin Fatima mai suna Gbenga yace matarsa bata da kirki ko kadan.
Ya ce ta dade ta na yi masa barazana da sai ta illa ta shi.
An daga sauraren karan zuwa watan gobe.