Kokarin da jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta yi na neman a dakatar Hon. Abdulmumin Jibrin daga jam’iyyar bai yi nasara ba, saboda matasa sun hana tabbatar da haka a ranar Larabar da ta gabata. Premium Times ta ruwaito cewa daruruwan magoya bayan dan majalisar ne suka cika sakatariyar jam’iyyar da ke Kano.
Hon. Jibrin, dan majalisar Tarayya daga jihar Kano, ya nemi shugaba Buhari da ya sauka daga mulki saboda dalili na rashin lafiya da kuma kasa aikatarwa ko gudanar da mulki a matsayin sa na shugaban kasa.
Wannan ne ya sa bayan sati daya da yin wannan kalami, sai uwar jam’iyyar APC reshen jihar Kano, su ka yanke shawarar dakatar da shi daga jam’iyya. To a ranar Laraba kuma kafin nan, gungun wasu matasa sun sha alwashin yi wa Hon. Jibrin kiranye daga wakilcin da yake yi masu na kananan hukumomin Bebeji da Kiru a majalisar tarayya.
Wakilin da ya ziyarci sakateriyar a lokacin da matasan da ba su so a hukunta Jibrin, sun yi ta reka kirarin “Sai Maliya.” Wani mai suna Sani Kaura, ya nuna fushin sa dangane da kokarin da ake neman yi na hukunta Jibrin, inda ya ce, abin da Jibrin ya yi ai shawara ce ya bayar, wacce ya ke da ‘yancin bayarwa a matsayin san a dan Nijeriya.
Shi ma Tasi’u Taro daga Bebeji, cewa ya yi, bai goyi bayan duk wani yinkuri na hukunta Hon. Jibrin ba. “Jibrin ya kawo mana ci gaba a mazabunmu, don haka tilas mu mara mara baya.” Yayin da Premium Times ta tuntubi Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano, Bashir Karaye, ya ce su babu wadanda suka hana su gudanar da taron su, sun ci gaba, ba su fasa ba.
A karshe ya ce za su dauki mataki bayan yin nazarin rahoton kwamitin gudanarwar ayyukan jam’iyyar.