Mataimakin shugaban marantar sakandare ya yi wa dalibar sa ciki

1

A yau Litinin ne alkalin Kotun Majistare da ke garin Minna jihar Neja ya ba da umarnin a tsare wani Mataimakin Shugaban makarantar Sakandare a bisa tuhumar sa da ake yi da yin lalata da wata dalibar sa mai shekaru 16 da haihuwa.

Mai Shari’a Fati Auna, ta tsare malamin mai suna Mohammed Kuyizhi, dan shekaru 51 da haihuwa, wanda ke makarantar Je-ka-ka-dawo ta sakandaren Tungar-Minna, bayan ya musanta cewa shi bai yi lalata da dalibar ba.

Alkali Fati Auna ta ce za’a ci gaba da shari’a ranar 5 ga watan Afrilu, 2017.

Dan sanda mai gabatar da kara, Abdullahi Maiyaki, ya shaida wa kotu cewa dalibar ce da kanta ta ce ya taba yin lalata da ita har sau uku a cikin ofishin sa.

“Wanda ake kara kan ba ta toshin naira 50 ko naira 100 a matsayin kudin mota zuwa gida duk lokacin da ya gama yin lalata da ita.” Inji mai gabatar da kara.

Ya kara da cewa wani malamin makarantar ne ya kai  rahoton wannan matsala ga kungiyar kare hakkin kananan yara, wato Child Right Protection Agency, bayan iyayen dalibar sun bayyana cewa an yi wa ‘yar su ciki.

Maiyaki ya ci gaba da cewa wanda ake tuhumar ya amince da cewa tabbas ya yi lalata da dalibar, amma bai zuba mata kwayar maniyyi da har za ta yi ciki ba.

Share.

game da Author