Manoman Rogo sun roki gwamnati da ta kara musu lokaci domin iya biyan basukan da suka karba bara

0

Hadaddiyar Kungiyar manomar rogo na Najeriya NCGA ta roki gwamnatin tarayya da ta kara wa manomanta lokaci domin su iya biyan bashin da suka karba daga hannunta.

Shugaban kungiyar Segun Adewumi ya fadi hakan ne da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai a Abuja.

Adewumi ya ce mafi yawa-yawan manoman rogo ba su sami yabanya mai kyau ba a shekarun da ya gabata saboda rikicin da su kayi ta fama da shi tsakaninsu da Makiyaya.

‘’Gwamnati ta ba mu wadannan kudaden ne domin mu noma rogo amma mun sami matsalar rashin siyar da amfanin gonan mu domin wadanda ya kamata su siya ba suu sami daman siya ba wanda hakan ya sa rogon duk suka rube.”

Bayan haka Adewumi ya ce yayin da gwamnati take kokarin dawo da wannan shirin na baiwa manoma bashin kudade domin noma kamata ya yi ta kawar da wasu matsalolin da manoman ke fama da su musamman a lokuttan da suka je karban bashin kudaden.

Ya kuma koka da yadda har yanzu gwamnati ba ta fara raba kayayyakin aikin noman bana ba duk da cewa damina ta fara kankama.

Daga karshe Adewumi ya roki babbar bankin Najeriya CBN da ta dauki manoman rogo cikin wannan shirin na ta na Anchor Borrowers’ Programme (ABP) a daminan bana.

Share.

game da Author