Majalisar Wakilai ta ba rundunar ‘yan sandan Najeriya awoyi 24 su dawo da takardun bayanai akan kasafin kudin 2017 da suka kwashe a gidan sanata Danjuma Goje.
Majalisar ta sanar da hakanne bayan tattaunawa da tayi a zauren ta yau.
Koda yake mafi yawan wadanda suka tofa albarkacin bakinsu akan maganar sun nuna fushinsu karara akan abin da jami’an ‘yan sandan suka yi a gidan Danjuma Goje.
Wani dan Majalisa mai wakiltan Kaduna, Barister Mohammaed Soba, ya ja wa majalisar kunne da su bi abin a hankali domin ba huruminsu bane suke neman cusa kansu a ciki.
Soba ya ce kowani fanni na gwamnati na da ikon da doka ta bata saboda haka dole ne su yi takatsantsan akan hakan.
Daga karshe sun kafa wata kwamiti da ta gaiyaci sifeton ‘Yan sandan kasa Ibrahim Idris ya zo yayi mata bayani akan abinda da ya faru.