Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta amince da dokar hana yin aure ba tare da shaidar yin gwajin cutar Kanjamau, Hypatitis, da sauran wasu cututtuka ba.
Dokar ta ce idan har aka kama wani mazaunin jihar ya yi aure ba tare da irin wadannan shaida ba za’a ci shi taran naira 100,000 ko kuma yayi zaman gidan yari na watanni shida.
Sannan kuma duk wani malamin asibiti da ya ba da shaidar karya zai biya taran naira N200, 000.
Majalisar ta mika dokar zuwa ga gwamnan jihar Nasir El-Rufai domin ta zama doka.