Lamidon Adamawa Barkindo Mustapha ya nada mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ‘Jagaban Adamawa’.
Lamido ya nada Osinbajo ne yau bayan wata ziyara da ya kai fadar sa yau.
Osinbajo ya ziyarci jihar Adamawa ne domin kaddamar da wata sabuwar titi da gwamnatin jihar ta gina.
Ya yabi gwamnatin jihar Adamawa akan irin ayyukan da ta ke yi wa mutanen jihar.