Kungiyar kula da aiyukkan jinkai na Najeriya ta sanar da cewa kudaden da take amfani dasu wajen ciyar da mutanen da ke fama da yunwa zai kare a wata Yuni.
Kungiyar ta ce sun shiga cikin halin karancin kudi ne a dalilin rashin wadata su da kudi kamar yadda wasu kungiyoyi sukayi alkawari tun a watan Fabrairu.
Majalisar dinkin duniya UN ta sanar a wata rahotan ta a watan Maris cewa tun a shekarun baya da dama wasu garuruwa kamar yakin arewa maso gabacin Najeriya da kudancin Sudan, Yemen da Somalia na fama da yunwa soboda rikicin da wuraren ke fama da shi.
Rahotan ya nuna cewa sama da miliyan hudu na mutanen Najeriya sun zama ‘yan gudun hijira saboda ayyukan Boko Haram kuma suna zaune a sansanoni dabam dabam a musamman jihar Barno. A dalilin haka suna bukatan taimakon abinci.
Rohotan ya nuna cewa mutane 43,800 daga cikin su na fama da matsanancin yunwa.
Peter Lundberg ya ce har yanzu basu cire tsammanin samun tallafin ba domin suna samun bayanai cewa akan dan sami matsaloli ne wajen wadanda zasu saki kudaden.