Wata kotu da ke zama a Kauyen Karmo, Abuja, ta yanke ma wani matashi dan shekara 22 hukuncin bulala 10 saboda kamashi da tayi da laifin sata.
Matashin mai suna Umaru, yana aikin gyaran wutan lantarki ne.
Matar da ta shigar da kara a kotun, Florence Auhioboh ta fada wa kotun cewa a ranar 6 ga watan Afirilu da misalin 4 na yamma Umaru ya saci dokin lokacin da ya zo aikin gyaran wutan lantarki a ungwan.
Alkali kotun Abubakar Sadiq ya yanke ma Umaru hukuncin bulala 10 akan laifin da ya aikata.