Kotu ta daure wani malamin makarata a Kano saboda yi wa dalibansa biyu fyade

0

Kotu a jihar Kano ta daure wani Shugaban makaranta mai zaman kanta har na tsawon shekaru 14 a dalilin fyade da yayi ma wasu dalibansa biyu yan shekaru 6 da 7.

Shugaban makaratar mai suna Ahmed Rufai ya zolayi yaranne zuwa ofishin sa inda daga nan ya aikata wannan mummunar aiki akansu.

Daya daga cikin yaran ta sanar wa iyayenta inda bayan an gudanar da bincike akai aka gano cewa yayi lalata da su.

Wani likita a asibitin Murtala da ke Kano bayan duba yaran da yayi ya tabbatar da anyi musu fyade.

A hukuncin da Kotu ta yanke ta ce bayan dauri shugaban makarantar zai biya iyayen yaran naira 50,000 kowannensu sannan zai biya jiha ita ma naira 50,000.

Share.

game da Author