Kotu ta bada belin Nnamdi Kanu

0

A yau ne mai shari’a Binta Nyako ta bada belin dan yakin neman kafa jamhuriyar Biafra, Nnamdi Kanu.

An bada belin sa a bisa sharuddan sai mutane uku sun tsaya masa, tare da kowanen su ya ajiye Naira Milyan 100 kafin a sake shi.

Belin dai an bada shi ne a bisa dalilin zuwa gida ya nemi maganin rashin lafiyar da ke damun sa.

Sauran sharuddan sun hada da cewa ba a yarda ya kasance cikin gungun jama’a sama da guda goma ba, sannan kuma ba a yarda ya tara gangami ko ya shiga cikin zugar wani gangami ba.

An kuma hana shi yin hira da ‘yan jaridu.

Share.

game da Author