Babbar kotun tarayya da ke Jabi, Abuja, ta hana wani roko da aka shigar a kotun cewa ta umarci babban Atoni Janar na Tarayya ya binciki tsoffin shugabannin hukumar hana al’mundahana da zambar kudade, EFCC.
Mai shari’a Abba-Bello Muhammed ne ya yi watsi da wannan batu na hana binciken, bayan ya saurari korafin da lauya Frank Tietie ya shigar. Mai shari’a ya soke korafin ne da ke cikin waka kara mai lamba M/4853/17 Da George Ubor ya shigar.
Ya ce babu wani dalili ko hujja da mai shigar da kara ya gabatar da zai sa mai shari’ar ya tilasta a binciki Nuhu Ribadu, Farida Waziri, Ibrahim Lamorde da kuma Ibarahim Magu.
Alkalin ya kara da cewa mai karar ba shi da wata hujja kuma ba shi iko a karkashin kowace doka da har zai nemi kotun ta tilasta wa Atoni Janar ya binciki tsoffin shugabannin EFCC din, ko kuma ta ce masa ga wadanda zai bincika.
“Na yi nazarin dukkan takardun korafin ku, amma hakan ba zai yiwu ba, har sai idan ku na da kwakwkwarar madogara daga dokar kasa, kafin a saurari wannan korafi na ku.”
Ya kara da cewa lauya mai zaman kan sa ba shi da hurumin da zai sa kotu ta tilasta wa Atoni Janar ya binciki shugabannin EFCC.