Keta haddin mata a tsakanin al’ummomin kasa Najeriya ya zamo ruwan dare musamman a wannan zamanin da kusan zai yi wuya ace wai an wayi gari har an kai yammaci ba’a sami rahoto akan an keta haddin wata ba ta hanyar yi mata fyade ko tauye mata hakkin ta na zama a tsakanin mutane.
Kungiyoyin kare hakkin mata da dama sun koka da hakan inda sau da yawa sukan mika kukan su ga gwamnati domin ta taimaka wajen ganin an kawo karshen irin wadannan tsautsayi da mata kan fada.
Abin yakan faru ga matan aure, matasa da kananan yara inda a dalilin haka sau dayawa wasu da dama kan rasa rayukansu.
Toma da matarsa Vicky
Kotun kara a Barkin-Ladi, jihar Filato ta yanke wa Toma hukuncin kisa ta hanyar rataya akan kashe matarsa Vikky da yayi.
Toma ya fusata ne bayan ya bukaci matarsa Vicky da ta zo gareshi a wannan lokaci amma Vikky ta roke shi da ya dan bata lokaci kadan ta huta gajiyar aikin gonar dake jikinta.
Hakan bai faranta wa Toma rai ba kawai sai harzuka ya shake ta har sai da ta daina numfashi.
Vicky dai nan take ta rasu.
Da yake yanke hukunci akan laifin Toma alkali kotun, Samson Gang y ace shima Toma zai bakunci lahira sanadiyyar abinda ya aikata wa matarsa ta hanyan rataya.
Charity Thomas
Charity Thomas ta riski ajalinta ne bayan saurayinta Sunday Umaru ya yi mata yankan rago a gidansa saboda sabani da suka samu akan wayan tarho.
Sunday Umaru ya kashe Charity ne saboda ta ki fada masa wanda ya kirata a waya.
Shi kuma gogan naka da ya fusata sai ya debe Charity ma mari. Abin baiyi mata dadi ba kawai sai ta caka wa kanta wukan da ke hannunta a lokacin saboda fushi.
Shiko Sunday sai ya ga cewa abinda ya fi mata shi ne ya aika ta lahira kawai, nanda nan ya fizge wukar ya yi mata yankan rago.
Simi da Justina Dusu
Daga kokarin samar da sulhu tsakanin Steven Luka da Justina wanda kanuwa ce a wurin Simi, Simi ta shafa lahira bayan Luka bai amince da uzurin da ita simi ta bad aba akan kanuwarta da dan da take dauke da shi a cikinta.
Justina dai ta hakikance cewa baza ta zubar da cikin da take dauke da shi ba wanda cikin Luka ne.
Shi kuma Luka ya sanarda ita cewa baya bukatar ta ajiye masa wannan cikin.
Justina da ‘yar uwarta sun nuna wa Luka cewa kada ya damu da yadda dan da Justina za ta Haifa domin zasu tabbata ya samu kula daga wajen sub a tare da ya kashe ko sisi ba.
Fadin hakan ke da wuya sai Luka ya dauko adda ya dinga sarawa Justina da ‘yar uwanta wanda hakan ya kai ga Simi ta rasa ranta.
Godwin Banchir
Godwin Banchir dan shekara 24 ya kashe mahaifiyarsa Saratu Banchir ‘yar shekara 65 da duka wai don bata amsa masa gaisuwar sa.
‘’Sanda na samu na dinga dukanta da shi amma ban san cewa hakan zai kai ga ajalinta ba.’’