An Karrama gidan Jaridar PREMIUM TIMES da kyauta mafi daukaka a aikin Jarida na kasar Amurka

0

Gidan Jaridar PREMIUM TIMES ta samu karramawa ta ‘Pulitzer Prizes’ na kasar Amurka saboda bincike da wallafa bayanai akan wasu jiga-jigan ‘yan Najeriya da na kasashen duniya da suke da dimbin dukiya da kamfanonin boye a wasu kasashen da ba’a biyan haraji domin guje wa biyan harajin arzikin da suka mallaka ga gwamnatocin kasashensu.

Gidan Jaridar PREMIUM TIMES tare da wasu kamfanoni 100 ne suka gudanar da wannan bincike da kuma wallafa bayanai akan badakalar da irin wadannan shugabannin da jiga-jigan ‘yan kasuwa na duniya suke aikatawa.

A kasa Nigeria, Gidan Jaridar Premium Times ne kawai ta samu wannan dama na shiga dandalin da irin wadannan bayanai ‘Panama Papers’ suke a ajiye da kuma zakula su don wallafawa a jaridar ta.

Kamfanonin da suka gudanar da wadannan bincike sun yi ne a inuwar Kungiyar ‘International Consortium of Investigative Journalists’ wanda ya hada da shahararriyar gidan jaridar kasar jamus dinnan mai suna Suddeutsche Zeitung, da wasu gidajen jaridu 100 a duniyar mu.

Binciken mai suna ‘Panama Papers’ ya ba da bayanai akan wasu shugabannin kasashen duniya da attajirai da suke boye dukiyoyinsu a wasu kasashen da ba’a binciken yadda kake gudanar da ayyukan kasuwancin ka da sanadiyyar arzikin ka.

Sunayin hakan ne domin gujewa biyan haraji da a kasashen su wand bincike ya nuna cewa saba wa dokar kasashen ne.

Binciken na ‘Panama Papers’ da akayi ya tona asirin kamfanoni da suke da alaka da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa 140 a kasashe 50 har da wasu shugabannin kasashe masu ci da wadanda suka sauka.

Binciken ya tona asirin wasu boyayyun manyan manyan Bankuna, da karbar cin hanci, da dai sauran su.

Gidan Jaridar PREMIUM TIMES ta wallafa labarai da ya kai 30 akan wasu jiga-jigan ‘yan Najeriya da suke da boyayyun ire-iren wadannan asusun a kasashen waje da ya hada da wanda shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da na matarsa. Da kuma irin wadannan boyayyun asusun da tsohon shugaban majalisar dattijai David Mark ya mallaka shima a irin wadannan kasashe.

PREMIUM TIMES ta rubuta labarai akan yadda tsohon gwamnan jiha Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha ya yi amfani da irin wadannan bankuna da ma’ajiya domin boye kudaden jihar sa da ya handame a lokacin da yake gwamnan jihar Bayelsa.

Shima gwamnan jihar Delta, James Ibori na daga cikin wadanda wannan bincike ta nuna irin watandar da yayi da kudin jihar sa kuma ya boye su a irin wadannan Kamfanoni.

Binciken da mukayi ya nuna yadda shahararren dan Kasuwannan Aliko Dangote, da dan uwansa Sayyu Dantata, da wasu kamfanoni mallakar Wale Tinubu, shugaban kamfanin mai na Oando da dai sauransu suka kauce sannan suka saba ma dokar kasa domin guje ma biyan haraji da boye dukiyoyin su.

Labaran ‘Panama Papers’ da muka wallafa a wancan lokacin ya nuna yadda shahararren faston nan mai suna TB Joshua, shugaban kamfani sadarwa na Etisalat, Hakeem Bello Osagie, Mike Adenuga, Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello da dai sauransu suma suka yi amfani da wannan shautacciyyar dama domin boye dukiyoyin su da guje wa biyan haraji akansu a irin wadannan kasashe da kamfanoni.

Shugaban gidan Jaridar PREMIUM TIMES Dapo Olorunyomi ya gode ma jama’a da irin gudunmuwar da suke ba gidan jaridar da amince mata da samar musu da labarai ingantattu.

A dalilin wannan nasara da gidan Jaridar PREMIUM TIMES ta samu na kasancewar ta cikin Jerin- gidajen jaridun duniya da sukayi fice wajen bankado harkallar da wasu shafaffu da mai sukeyi da kudaden jama’a a kasashen duniya da kauce ma biyan haraji a kasashen su, jama’a da Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun jinjina ma wannan gidan Jarida akan wannan aiki nata.

Da yawa sun aiko wa gidan jaridar da sakon sambarka da na fatan Alkhairi akan hakan.

Karanta labarin a shafin mu na Turanci a nan: Celebrations at PREMIUM TIMES as Panama Papers wins Pulitzer Prize

Share.

game da Author