KANJAMAU: Yaduwar ta ya karu a sansanonin ‘yan gudun Hijira dake jihar Barno

0

Shugaban hukumar kula da cutar kanjamau na jihar Barno BOSACA Barkindo Saidu ya sanar da cewa sama da mutane 3,800 mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar ne suka fama da cutar kanjamau.

Saidu yace an samu wadannan bayanai ne bayan gwajin da akayi wa mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira 15 a jihar tsakanin watan Janairu zuwa Maris na 2017.

Bayan haka kuma ya sanar da cewa bisa ga binciken da hukumar kidaya ta kasa ta yi, akalla mutane 108,000 ne ke dauke da cutar a fadin jihar.

Cikin mutane 3,800 da aka tabbatar suna dauke da cutar an samu yara kanana 70 da su ma suna dauke da shi.

Saidu ya kuma kara da cewa a jihar gaba daya an sami sabbin rahotanni na mutane da suka kamu da cutar da ya kai 18,101 wanda a haka mutane 9,438 ne kawai suke karban magani domin samun sauki ga cutar.

Matsalolin da BOSACA ke fuskanta a jihar

1. Rashin cikakken shiri domin kawo karshen yaduwar cutar kanjamau a jihar.

2. Kadan daga cikin mutanen da ke dauke da cutar ne ke samun magani.

3. Rashin isassun cibiyoyin kiwon lafiya da masu dauke da cutar zasu dinga karban maganin.

4. Nuna halin ko in-kula da gwamnatin jiha da na tarayya ke nuna wa musamman wajen wadata hukumar da kudade da tallafi.

5. Rashin samun isasshen tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu.

Daga karshe Saidu y ace ya sake rubutawa gwamnatin jihar domin ta basu hadin kan da suke bukata sannan kuma ya roki sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su kara yawan tallafin da suke basu domin ganin an samu nasara akan wannan cuta .

Share.

game da Author