Kungiyar Kiristocin Najeriya ta yi Kira ga gwamnatin Tarayya da ta dai na fakewa da wadansu abubuwa domin boye gazawarsu kan kawo karshen rikicin Fulani Makiyaya da mazauna wasu garuruwa a fadin Kasa Najeriya.
Dayake hira da manema labarai a shirin da kungiyar ta keyi na fara yin wata taron gangami na kwana biyar a Abuja shugaban shirya taron kuma Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya Samson Ayokunle yace ayyukan Fulani a wasu sassan kasa Najeriya ya nuna cewa matsalar ya fi karfin gwamnati.
“A makon nan kawai Fulani sun kashe mutane 30 a kauyukan kudancin Kaduna.”
“ Ashekarar da ta gabata gwamnati ta sanar da kafa wata rundunar soji ta musamman domin yaki da masu tada zaune tsaye a yankunan amma duk da wannan shiri na gwamnati an ci gaba da samun kashe-kashen mutane a yankunan.
“ Irin yadda jami’an tsaro suka yi maza-maza wajen kamo wadanda ke da hannu a rikicin Ile-Ife bamu ga haka ba a na Fulani makiyaya da suka addabi mazauna garuruwa da dama a kasar nan.
“ Muna kira ga gwamnati da su kara kaimi wajen ganin an kawo karshen wannan kashe kashe da Fulani makiyaya sukeyi domin a gaskiya an kaimu makura yanzu.”
“ Muna jinjina wa gwamnati da sojojin Najeriya kan kokarin da ta keyi wajen ganin an kawo karshe ayyukan Boko Haram a Kasa Najeriya.
Ya kuma ce gwamnati ta duba yadda take raba mukamen gwamnati da lura da daidaita rabon ga addinan kasarnan yadda ya kamata.