KADUNA: Jam’iyyar APC za ta iya shan kayi a zaben gwamna a 2019

0

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Kwamared Shehu Sani yace alamu ya nuna cewa idan har gwamnan jihar Mal. Nasir El-Rufai ya ci gaba da irin mulkin da yake gudarnawa na kin Jama’a a jihar to fa jam’iyyar za ta sha kashi a zaben gwamna a 2019.

Shehu Sani yace gwamnan sam baya tare da mutanen jihar, abin da ya ga dama kawai ya keyi wanda kuma ya shafi talakawan jihar ne.

Ya fadi hanne da yake sauraren kukan ‘yan Kasuwan Barci da ke unguwan Tudun Wada da suka kawo masa ziyara da kukan neman ceto cewa gwamnan El-Rufai zai rusa kasuwar.

“Irin abubuwan da yake yi a jihar ya sa mutane da yawa suna gudun jam’iyyar a jihar. Da yawa da ga cikinsu suna cikin ta ne saboda Buhari.

“ Duk ayyukan da gwamnatin jihar takeyi ba na jama’a bane kuma idan har ta ci gaba da haka to jam’iyyar za ta sha kasa a zaben gwamna a jihar.

“ Shirye-Shiryen gwamnatin Jihar a na yin su ne domin wasu mutane ‘yan kadan amma ba don ya amfani dimbin jama’ar jihar ba.

Shehu sani ya ce a gaskiya rusa kasuwa kamar Kasuwar Barci wanda ke da shaguna sama da 4,800 zai san ya mutane da yawa cikin halin ha’ula’i.

Yan kasuwan sun koka da wannan shiri na gwamnatin jihar sannan sun ce idan har aka ci gaba da wannan shiri za su fada halin takura domin sama da mutane 30,000 ne suke amfana da Kasuwar.

Share.

game da Author