JIGAWA: A shirye muke da mu rasa rayukan mu da a kwace mana gonaki a ba Mista Lee

0

Shawarar da gwamnatin jihar Jigawa ta dauka na kwace filayen manomar wasu kauyukan jihar dake kananan hukumomin Suletankarkar, Gagarawa, Taura, da Garki ya jawo cece-kuce tsakanin manoman yankin da gwamnatin jihar.

Sama da mutane 150,000 ne wannan shire na gwamnati zai shafa wanda zai yi sanadiyyar salwantar filayen manoman yankin da ya kai fadin hekta 12,000.

Gwamnatin Jihar Jigawa da wani dan kasuwa dan kasar Sin wato China mai suna Mr Lee sun amince da shi Lee din ya mallaki filayen domin gina kamfani a jihar.

Mazauna garin sun koka da wannan shiri matuka inda suka sanar wa Gidan Jaridar Premium Times cewa filayen da gwamnati take kokarin kwace wa daga hannunsu filaye ne da suka gada daga kakanninsu.

Mazauna garuruwan sunce ba za su yarda gwamnati ta nuna musu irin wannan fin karfi ba. Za su tsaya tsayin daka domin ganin hakan bai faru ba ko da za su rasa rayukansu ne.

Wani mazaunin kauyen Gaya Muhammed Danu ya ce ‘’A rude muke sannan dukkan mu muna cikin zullumi akan wannan shiri da gwamnati ta yi akan filayen mu.

“ Wannan filaye dai mun gaje sune da ga iyaye da kakanni. Muna noma wadannan filaye duk shekara sannan da abinda muka noma ne muke ciyar da kan mu, mu aurar da ‘ya’yan mu sannan mu wadata kan mu da abubuwan da muke bukata.

Danu yace gaba dayan su a wadannan garuruwa da ake kokarin kwace musu filaye sun mara ma wannan gwamnati baya dari bisa dari amma da wannan bakin ciki za su saka musu.

A madadin mutanen yankin, dan majalisa Sani Zorrro ya mika wannan batu a majalisar Wakilai kuma tuni majalisar ta umurci wata kwamitinta da ta binciki maganar ta kuma kawo mata bayanai akan abin da ta samo.

Karanta labarin a shafin mu na Turanci a nan: http://wp.me/p2LdGt-Xl3

Share.

game da Author