Sarki Kano Muhammadu Sanusi ya koka da yadda gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya jibanta cutar Sankarau da ya addabi mutanen jihar sa cewa wai laifukan da mutane ke aikatawa ne ya sa Allah ya sauko da wannan cuta a kansu.
“ Wannan magana da kayi bai yi daidai da Karantarwan Addinin Musulunci ba.
“ Idan baka da maganin rigakafi ka ce baka da shi, sai kaje ka nemo wa mutanen jihar ka kawai.” Sanusi yace.
Har ila yau Sarkin ya koka da yadda shirya fina-finan Hausa yake neman ya bar jihar Kano Kwata-kwata zuwa jihar Kaduna saboda tsauraran dokoki.
Sarkin yace duk da hakan bai yi masa dadi ba amma ganin cewa Kaduna ne akalar ta karkata zuwa Abin farin ciki ne.
Yace da an amince da mara wa masu harkar shirya fina-finai da ba karamin ci gaba za’a samu ba musamman ga matasan arewacin Najeriya.
Yace daya da ga cikin abubuwan da suka sa yankin arewa bata samu ci gaban da ya kamata ba zuwa yanzu shine dalilin ra’ayi da muke dashi na kin sabon abu a gari.
Hakan ya sa an bar yankin a baya.
Sarki Sanusi Ya fadi hakan ne a taron bunkasa kasuwanci da masana’atu da gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya.
Ya ce matsalolin Arewa su na da dimbin yawa. Nan da nan ya fara bayani dangane da matsalar yadda gwamnoni ke tafiya kasar China da sunan nemo masu zuba zuba jari, amma a karshe sai su bige da ciwo bashi. ‘’Ko kuma ka ga an shigo da injina daga Chana, ma’aikata daga Chana, komai hatta direbobin motoci ma daga Chana.”
Sarkin ya kuma bai wa dimbin masu sauraron sa dariya, yayin da hadimin sa ya gyara masa alkyabbar sa, ganin cewa ta na sauka daga kan kafadun sa. Mai Martaba ya ce, “Kada ku damu, alkyabbar ‘yar Chana ce.”
Sarkin ya ce ba a ci gaba sai ana zuba jari domin kafa masana’antun da za su gina al’umma. Sai dai kuma ya ja hankali cewa ci gaba na zuwa ba ta hanyar yawan ciwo bashi ko kashe kudaden gwamnati ba.
Da ya koma kan matsalar Arewa, ya ce talauci da rashin ci gaba da rashin lafiya da rashin ilmi sun yi wa yankin katutu. Ya buga misali da jihohin Yobe da Barno, inda ya ce wadannan jihohi su biyu, sun fi kasashen Nijar, Kamaru da Chadi fama da talauci da mummmunar fatara.
Dangane da matsalar da ke addabar al’ummar Arewa, ya ce nauyin kowa ne ya fito mu fada wa juna gaskiya. Mu na da milyoyin yara da ba su zuwa makaranta, mu na da matsalar ilmi da mtsalar lafiya. Tilas sai an tashi tsaye an sake zuba jari a wadannan fannoni.
“Me ya sa al’umma mai irin wannan yawan da ba ta da ilmi, ba ta iya ciyar da kanta kuma talauci da matsalar lafiya da jahilci sun yi mata katutu? Idan haka ne me yawan ya amfana kenan? Ba yawa ba ne abin tutiya, sai yawan abin da za mu amfana wa kan mu wajenn ci gaban mu a matsalar rayuwar mu.”
“Yanzu ku duba ku gani. Idan mu na da yara milyan biyar da ba su zuwa makaranta, to a lokacin da za ka gina makarantu domin samar wa ga dubu dari biyu da hamsin a cikin su, kafin ma ka gama da su an sake samun wasu rabin milyan kuma.”
A karshe ya yi kira da a daina amfani da addini ana kashe-kashen juna. Inda Sarkin ya yi nuni da cewa tilas ne kowa ya sani cewa duk yawan ilmin mutum ko a wane addini ya ke, aikata kisa laifi ne, ba addini ba ne.
Ya yi fatan samun nasar shirin, kuma ya yi kira da kada a bari shirin ya shiririce bayan kammala mulkin gwamnatin El-Rufai.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=D_t27-qlExI&w=560&h=315]
Discussion about this post