Ina tare da Magu da ayyukan da yake yi a hukumar EFCC 100 bisa 100 –Inji Ribadu

0

Tsohon shugaban hukumar EFCC Mal. Nuhu Ribadu ya karyata rade-radin da ake ta yada wa a wasu kafafen yada labarai cewa wai yana adawa da shugabancin Ibrahim Magu da ayyukan da hukumar EFCC ta ke yi a kasa Najeriya.

Nuhu Ribadu ya fadi hakan ne a shafinsa na twitter inda ya yi kira ga ‘yan Najeriay da su yi watsi da irin wadannan labarai domin ba daga bakinsa ne ba suka fito.

“Wasu ne da basu da aikin yi suke fitar da irin wadannan zantuka domin bata mini suna.”

“Ina tare da shugaban hukumar Ibrahim Magu kuma ina jinjina ma ayyukan da sukeyi 100 bisa 100.”

Share.

game da Author