Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin sa ta dauko hanyar magance matsalar tattalin arzikin kasa da a ka shiga.
Buhari ya fadi hakanne a jawabin sa da yayi a wurin kaddamar da shirin farfado da tattalin arzikin kasa yau a Abuja.
Ga cikakken fassarar jawabin shugaba Muhammadu Buhari
Kamar yadda duk mu ka sani ne, wannan gwamnati ta gaji dimbin matsaloli daga gwamnatin da ta gabata. Yakin neman zaben da muka yi ya ta’allaka ne wajen gano irin matsanancin halin da Najeriya ta samu kan ta a wancan lokaci, tare da bukatar kawo canji mai amfani ga al’umma.
Har yanzu a haka mu ke, kuma mu na nan a kan turbar cika alkawurran da mu ka dauka a lokutan yakin neman zabe wajen canja alkiblar Najeriya daga karkatattar hanyar da ta ke a kai.
Mu na kan turbar tabbatar da mun yi nasara a kan fannonin nan uku da muka yi alkawarin magancewa, wato matsalar tsaro, dakile cin hanci da wuwurar kudade da kuma sake farfado da tattalin arzikin kasar nan.
A yau harkar tsaro ta inganta a yankin Arewa-maso-gabas da sauran sassan Najeriya, fiye da yadda mu ka same ta da farkon hawan mu mulki.
Dangane da kokarin mu na yakar rashawa kuwa, kowa ya sani Jami’ar tsaron mu na ci gaba da gurfanar da mutane da yawan gaske. Don haka nasarorin da mu ka samu a wadannan fannoni biyu, a fili su ke kowa na iya ganin su.
Ina tabbatar wa dukkan ‘yan Najeriya cewa mun dauko hanyar magance matsalar tattalin arzikin mu kamar dai yadda mu ka jajirce wajen samun nasarorin shawo kan matsalar tsaro kan ‘yan ta’adda da kuma cin hanci da rashawa.
Wannan shiri na farfaro da tattalin arziki ta tattaro dukkan fannonin aikin noma da abinci, lantarki, sufuri, masana’antu da zuba jari a fannin inganta rayuwar jama’a.
Don haka nan da shekara uku, wato cikin 2020, mu na da yakinin samun ci gaban tattalin arziki da kashi 7℅ cikin 100.
Burinmu a saukake shi ne samar da kayayyaki na cikin gida tare da habbaka masu kananan masana’antu.
Ba wai kawai za mu fitar da Najeriya daga matsin tattalin arziki kawai ba, har ma sai mun Dora ta a kan turba dawwamamma mai ingantaccen tattalin arziki.
Mun kudiri aniyar canja Nijeriya daga kasa mai dogaro da shigo da komai daga waje, zuwa kasa mai samar wa kanta komai da kan ta.
Tilas sai fa mun zama kasa mai noma dukkan abincin da ta ke ci. Kuma mu mike tsaye wajen kara samar wa naira daraja.
Tsarin nan da na kaddamar a yau, an shimfida shi ne a kan abin da a matsayin mu na gwamnati mu ka sha alwashin samar da dama da yanayi mai kyau wajen samun nasarar kasuwanci.
Don haka ne na ke kira ga gwamnatocin jihohi da su bi sawu wajen kwaikwayar wannan shiri na infanta tattalin arziki.
Ina kira ga dukkan ‘yan Nijeriya ku fito mu yi aiki tare domin mu tabbatar da samun nasarar kai wa gacin wannan gagarimin shiri.
An yi nazarin fito da wannan shiri ne ta hanyar tuntubar duk wasu masu ruwa-da-tsaki da suka hada da Majalisar Tarayya, gwamnonin jihohi, ‘yam kasuwa, kungiyoyin kwadago, masana da sauran su.
A karshe, ina jinjina wa ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare, saboda samun nasarar fito da wannan daftari na kawo ci gaba.
Sannan kuma ina godiya ga kwamitin sa-ido kan tattalin arziki a karkashin shugabancin Mataimakin Shugaban Kasa, wanda wannan kwamiti ne ya bi diddigin rubuta wannan daftari.
Ina mai farin cikin gabatar da Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar nan domin ‘yan Nijeriya su yi amfani da shi, haka abokin mu da kuma abokan huldar kasuwancin mu, su kuma saka mu hanya wajen kara nuna mana hoton bayan wannan shiri nan da zuwa shekara hudu masu zuwa.