Shugaban hukumar kula da kudaden rigakafi na kasa NIFT, Ben Anyene ya koka da yadda kasa Najeriya ke fama da matsalar karancin alluran rigakafin cutar sankarau.
Ya fadi hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Anyene ya ba da bayanai akan matsalolin da ake fama dashi na karancin alluran rigakafi a Kasa Najeriya.
Kamar yadda bincike ya nuna, tsohon shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko NPHCDA, Ado Bayero ne ya kafa wannan hukumar domin kasa Najeriya ta iya shirya aiyukkanta yadda ya kamata wajen samar da allurar rigakafi da kuma kudaden da za a bukata domin siyansu.
Anyene ya ce a yanzu haka kasa Najeriya na matukar bukatan alluran rigakafin cutar sankarau domin tun da cutar ta bullo a watan Nuwamban 2016 cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 700.
Ya ce kasa Najeriya ta sami kanta ne a irin wadannan matsaloli saboda rashin mai da hankali da wadanda hakkin kula da samar da shirye shiryen da zai sa kasa ta kauce ma fada wa irin wannan matsala musamman ganin an san da cewa akwai yiwuwar bullowar cutar a lokacin rani.
Ya kuma kara da cewa gwamnati na ta cewa kasar Britaniya za ta aiko da alluran rigakafi amma idan aka duba kasan Britaniya bata da cutar sankarau a kasarta saboda irin shirye-shiyen da kasar ta yi wajen ganin cewa ta kawar da cutar tuntuni wanda ba hakan yak e a kasa Najeriya ba.
Anyene ya shawarci kasa Najeriya da ta dage wajen tsara shirye-shiryen da zai taimaka wajen kawo karshen cutar .
Ya ce yanzu haka samun alluran rigakafin na da wahala saboda alluran na daukan akalla tsawon watanni shida bayan an biya kudaden siyansu daga kasashen waje.
Bincike ya nuna cewa adadin yawan alluran da kasa Najeriya ta samu ya kai 500,000 sannan kuma tana jiran wasu alluran da ya kai 823,970 daga kasar Britaniya.
Anyene yace idan aka kwatanta adadin yawan alluran da mutanen kasar gaba daya suke bukata za a gane cewa akwai karancin alluran rigakafi domin jihar Zamfara kadai na bukatan alluran rigakafin cutar Sankarau da ya kai miliyan uku wanda 300,000 ne kawai suka iya samu zuwa yanzu.
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole yace bullowar cutar sankarau a kasa Najeriya ya sa dole ya kwabi jami’an ma’aikatarsa kan su kara daura damara sannan su dage domin ganin ba’ a sake yin sakaci ba game da yaduwar irin wannan cuta a gaba.
Ya kuma ce kasan za ta bukaci kudade masu yawa a shekaran 2026 wajen kawar da cutar saboda a kowace shekara kasan na samun haihuwan yara jirajirai daya kai miliyan 8.
Adewole ya kuma roki alfarmar hukumomin da suke tallafa wa Najeriya kamar hukumar kiwon lafiya na majalisar dinkin duniya WHO, hukumar kula da bada tallafin na alamuran yara UNICEF,da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu kamar su Rotary,kungiyoyin da suke kasashen Canada, Japan da kuma sauran da su kara yawan talafin da suke bawa kasa Najeriya.
Shi kuwa shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko NPHCDA Faisal Shuaib ya ce ya kamata kasa Najeriya ta sami kwararrun mutanen kididdigar kudi domin su kididdige kudaden tallafin da fannin kiwon lafiya take samu.
Ya ce hakan zai taimaka wajen samun Karin tallafin da kuma kima a idanuwar hukumomi da kungiyoyin da suke ba da tallafi.