Idan da zunubi na sa a kamu da cutar Sankarau da kusan duka ‘yan siyasa sun kamu – Inji Sanata

0

Sanata mai wakiltan jihar Bayelsa Ben Bruce ya zolayi gwamnan jihar Zamfara kan cewa da yayi wai aikata zunubai ne da mutane su keyi ya sa ake ta fama da cutar Sankarau a wasu sassan kasar nan.

Sanatan yace bai yarda da abinda gwamna AbdulAziz Yari yace ba wai “aikata laifi ne da mutane sukeyi ke kawo cutar Sankarau.”

“ A na kama cutar Sankarau ta dalilin yaduwar kwayar cuta ne ba don an aika ta laifi ba.

“Idan zunubi ne ke kawo cutar Sankarau da dukkan mu ‘yan siyasa mun kamu da cutar.

Share.

game da Author