Hukumar zabe za ta fara yin rijistar sabon katin Zabe ga wadanda basu dashi

0

Hukumar zabe INEC ta sanar da fara yi wa wadanda basu da katin zabe rijista, musamman wadanda a wancan lokacin da akayi basu kai shekarun yin zabe ba sai yanzu.

Za’a fara yin rijistan ne daga ranar 27 ga watan Afrilu inda zai ci gaba har zuwa wasu ‘yan watanin shekara 2019.

Sakataran hukumar Aliyu Bungudu ne ya sanar da hakan a taron da aka shirya wa masu ruwa da tsaki akan harkar Zabe a garin Minna.

Bungudu ya kara da cewa hukumar baza ta jinkirta sauke nauyin da ke rataye a kanta ba na tabbatar da ganin kowa ya sami damar yin zabe sannan kuma ya yi kira da ayi kokarin fitowa domin yin rijistan.

” Za mu dakatar da yi wa mutane rajistan katin zabe gab da a fara zaben 2019.”

Ya kara da yin kira ga duk wadanda suka yi rajistan a shekarun baya amma ba su karbi ainihin katin zaben nasu ba su zo su kar ba yanzu.

Share.

game da Author