Hukumar Kula Da Abinci Ta Duniya, ta bayyana cewa ta ware zunzurutun kudi har dala miliyan 65 domin taimaka wa manoman da rikicin Boko Haram ya kassara musu harkokin su.
Hukumar ta ce za ta raba wannan tallafin ne ga manoman jihohi uku da Boko Haram ya fi yi wa illa, wato Adamawa, Barno da Yobe.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin wakilin hukumar na Najeriya, Nouron Macki, wanda ya bayyana haka a wata ziyarar gani-da-ido da ya kai Maiduguri, babban birnin jihar Barno a ranar Alhamis da ta gabata. Ya shaida wa ‘yan jarida cewa hukumar sa za ta raba wannan tallafin ne a karkashin wani shiri na musamman don agaza wa manoman da Boko Haram suka kassara.
Nouron Macki ya kara da cewa, shirin zai ta’allaka kacokan ne wajen farfado da noma da kuma rayuwar wadanda ke sasasanonin gudun hijira bayan komawar su yankunan su na asali.
Ya kuma ce an kuma tallafa wa manoma dubu dari biyu domin sake farfado da kiwon dabbobi da kuma kiwon kifaye da noma.
Daga cikin wadanda tuni aka taimaka wa din, akwai magidanta dubu arba’in da takwas a jihar Barno, wadanda suka amfana da shirin noman rani sai kuma wasu 2160 da suka amfana a shirin noman damina.
Macki ya ce, “Zuwa yanzu dai mutane dubu dari da arba’in ne suka amfana daga shirin noman rani, yayin da wasu dubu dari da arba’in da shida suka amfana da shirin tallafi na damina a jihohin Adamawa, Yobe da Barno.”