Gwamnatin Tarayya ta tallafawa jihar Sokoto da alluran rigakafin cutar Sankarau

0

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya sanar da cewa gwamantin tarayya ta tallafawa jihar Sokoto da gudunmuwar alluran rigakafin cutar sankarau miliyan 1.8.

Ya sanar da hakan ne a garin Dange dake karamar hukumar Shuni a wajen kaddamar da shirin bada allura rigakafin cutar sankarau wa mutanen garin.

Kwamishanan kiwon lafiyar jihar Balarabe Kakale wanda ya wakilci gwamnan ya ce sun kawo ma’aikatan bada alluran rigakafin 300 wanda za su yi aikin a kananan hukumomi 23 a jihar.

” Kokari muke mu ga cewa mun kawar cutar sankarau a jihar kuma muna matukar farinciki akan nasarorin da muka yi ta samu tun bayan barkewar cutar a kasa Najeriya wajen ganin mun wadata mutanen jihar da rigakafin cutar.

Tambuwal ya jinjinawa gwamnatin Najeriya, sarakunan gargajiya, shugabanin addini da manyan gari da su taimakawa gwamnati wajen fadakar wa mutanen garuruwansu mahimmancin yin rigakafin.

Share.

game da Author