Gwamnatin Jihar Kaduna ta rusa gidan mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyar Arewa maso Yamma, Inuwa Abdul’Kadir da ke cikin garin Kaduna.
Inuwa Abdul’Kadir yace ya san za’ayi haka ko domin irin rikon da El-Rufai yake dashi a zuciyar sa tun bayan kokarin sasanta shi da Shehu Sani da yayi.
“Domin gwamnan ya fadi cewa zai aikata hakan a gaban wasu gwamnoni shida.
“ Abin bai bani mamaki ba saboda na san El-Rufai zai aikata haka, amma ba zan ce komai ba tukuna domin maganar na kotu yanzu.
Hukumar kula da tsara birani na jihar Kaduna ne ta rusa gidan Inuwa Abdulkadir yau a garin Kaduna.