Gwamnatin Jihar Kaduna ta maka dan jaridar Vanguard Biniyat Luka saboda Zargin rubuta labarin karya da yayi cewa wai an kashe wadansu daliban kwalejin koyan aikin malunta dake gidan waya, kudancin Kaduna.
Cikin abubuwan da ake tuhumar Biniyat akai shine labarin da ya rubuta a watan Janairu cewa wai wasu makiyaya sun yi garkuwa da wadansu daliban makarantar biyar inda suka kashe su.
Bayan an gudanar da bincike akan haka an gano cewa wani abu makamancin hakan bai faru a jihar ba har da inda marubucin yace ta faru.
Gwamnati ta kai Biniyat kara Kotu tana tuhumar sa akan ta da zaune tsaye da yayi a jihar a dalilin wannan labari da ya rubuta.