Gwamnatin Jihar Kaduna ta Kaddamar da sabuwar fasaha domin sanin ayyukan da gwamnati ta keyi

0

Kwamishin Kasafin Kudi na Jihar Kaduna Mohammed Sani ya yi bayanin wata sabuwar fasaha da gwamnatin jihar Kaduna ta kirkiro da ta ke amfani ta wayar sadarwa inda da zarar ka saka shi a wayar ka zai dinga nuna maka ayyukan da gwamnatin jihar ta keyi a unguwar ka ko kuma unguwar da ke kusa da akai.

Mohammed Sani yace ofishinsa ta kirkiro wannan fasaha ce domin tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na sane da su a duk abubuwan da ta sa a gaba.

“Za ka samu wannan fasa ce da muka kirkiro da zarar ka shiga kasuwar ‘Google Play store’ sai ka nemi ‘Kaduna Citizen Feedback’ zai fito ma ka nan take.

“Kan saka shi a wayar ka zai nuna maka irin ayyukan da gwamnati take yi a kusa da kai, sunan dan kwangilar da yake aikin da matsayin aikin a wannan lokaci.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron, gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yace Gwamnatin jihar Kaduna zata ci gaba da samar wa mutanen jihar da abababn more rayuwa kamar yadda ta dauki alkawari.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi a nashi jawabin ya yi kira ga gwamnonin Arewacin Najeriya da suyi koyi da irin ayyukan da gwamnan jihar Kaduna yake yi a jihar sa.

Shi kuma shugaban Jam’iyyar APC John Oyegun ya jinjina wa gwamna El-Rufai ne akan irin wadannan ayyuka da yake gudanarwa a jihar.

“ El-Rufai ya na yin abubuwan da jam’iyyar mu ta APC tayi alkawarin samar wa jama’a. Na sani cewa da zaran ya kammala wadannan ayyuka da ya sa a gaba jihar Kaduna za ta zama wata Alkaryar a zo a gani.

Share.

game da Author