Gwamnati za ta shata wa makiyaya burtaloli masu tsawon kilomita 6000

0

Ranar Juma’ar nan ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta ware burtaloli ha tsawon kilomita 6,000 domin makiyaya shanu a cikin 2017. Ko’odinata na hanyoyin burtali mai kula da kiwon shanu da makiyaya na kasa, Muhammaed Bello ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN wannan jawabi.

Ya bayyana cewa za su fara buge burtaloli na kashin farko na gwamnatin tarayya, yayin da jihohi da kuma kananan hukomomi za su bude na su daga baya. Ya ce ba za a samar da burtalolin ga jihohi daidai da kowace ba. Jihar Bauchi ce za a ware wa burtaloli har na tsawon kilomita 200, ita kuma jihar Filato za ta samu na tsawon kilomita 50.

Ya kara da cewa za a kara inganta tsarin haihuwa na shanun yadda kowace saniya za ta rika samar da madara lita 25 a kowace rana, maimakon lita 1.5 a kowace rana da suke samarwa a yanzu.

Ya kuma ce wannan tsarin fito da burtali, zai hana makiyaya su rika kutsawa cikin gonakin manoma su na cinye musu amfanin gona. Ya kuma ce an fito da tsarin ta yadda nan gaba ba za a rika bi ana sayar da burtalolin ba kamar yadda aka bi duk aka sayar da burtalolin da aka killace tun a cikin 1962.

Bello ya ci gaba da bayyana cewa rijiyoyin burtsatse, madatsun ruwa da filayen kiwo na dajin gwamna, duk za a raba su ga makiyaya ba da dadewa ba. Ya ce wadannan wurare duk su na nan, amma makiyaya sun watsar da su ne sakamakon yawan kaura da su ke yi daga wannan wuri zuwa wancan.

“ A wannan lokaci, gwamnatin tarayya za ta ware fili mai hekta 50 a shiyyoyin makiyaya domin samar da wuraren ingata makiyaya. Za a yi amfani da shiyyoyin a matsayin wuraren inganta noma, kiwo da kuma samar da irin shuka.”

Share.

game da Author