Gwamnan jihar Bauchi ya gaiyaci Efe zuwa wurin shakatawa na Yankari

1

Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya gaiyaci wanda ya samu nasarar cin gasar ‘Big Brother Naija’ Efe (Ejeba Michael Efe), zuwa wurin shakatawa na ‘Yankari Games Reserve’ wanda ke jihar bayan nasaran da ya samu a gasar da aka kammala a makon da ya gabata.

Gwamnan jihar Bauchi ya mika sakon gaiyatar ne ta shafinsa na twitter.

Efe ya sami nasara a gasar sakamakon yawan kuri’un da ya samu.

Ya kuma sami kyautar tsabar kudin na naira miliyan 25 da sabuwar motar KIA Sorrento SUV.

Dajin shakatawa na Yankari na daya daga cikin wuraren shakatawa da suka shahara a kasa Najeriya.

Share.

game da Author