Gwamnan jihar Adamawa Jibirilla Bindow ya koka da yadda ake wancakalar da jihar sa wajen nada mukaman gwamnati a kasa Najeriya.
Gwamnan yace idan har gwamnatin tarayya batayi komai a kai ba zai iya ficewa daga jam’iyyar APC.
Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Abdulrahman Jimeta ne ya fadi hakan a gaban gwamna Bindow, kuma bai han shi ba a lokacin da suke ganawa da shugabannin jam’iyyar na shiyar Arewa Maso Gabas a Yola.
Jimeta yaba tawagar Sako zuwa ga uwar jam’iyyar ta kasa cewa “ Muna nan muna yi mata biyayya amma fa ta sani cewa ko addine ne mutum ya gaji dashi yakan iya canza shi.
“ Ku gaya musu cewa bukitin mu ya fara cika, musamman ganin cewa basu damu da halin da muke ciki ba, mu ne sojojin jam’iyyar kuma mune ya kamata mu amfana da jam’iyyar amma idan har suka ki yin komai a kai za mu canza sheka zuwa jam’iyyar adawa.
“Gwamnatin tarayya ba ta ne man shawaran mu anan idan za tayi nade-naden ta musamman wanda ya shafi jihar Adamawa.”
Gwamnan jihar Jibirilla Bindow ya yabi shugaban Jam’iyyar ta su na Kasa John Oyegun sannan yace za su ci gaba da yi wa jam’iyyar biyayya.