El-Rufai da Saraki ne suka dakile shiri na na zama mataimakin Buhari – Inji Tinubu

0

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jamiyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki ne suka hanashi zama dan takaran mataimakin shugaban kasa a 2015.

Ya ce a wancan lokacin sun gama shirya komai nasu duk da cewa El-Rufai na tare da su amma ya yi mishi yankan baya ya zagaya ya na bin ‘ya’yan jam’iyyar CPC a wancan lokacin domin su ki amincewa da wannan shiri.

Dukkan su suna cewa wai ba zai yiwu a ce wai an tsayar da musulmai biyu a matsayin ‘yan takara ba.

“ El-Rufai yana ta yin haka ne domin ya na kokarin cusa abokinsa Tunde Bakare domin ya zama dan takaran mataimakin shugaban kasan.

“Da shi El-Rufai da Saraki suka bi baya suna ta zuga Buhari akan yaki wannan shiri domin wai Kiristocin Arewa ba za su zabi jam’iyyar ba idan akayi musulmai biyu.

“ Gwamnonin PDP da suka shigo jam’iyyar APC a lokacin suna daga cikin wadanda suka hargitsa komai saboda wuri da muka basu daga shigowarsu jam’iyyar APC din. Saboda kaunar da ke Tsakani na da Buhari da irin amincewa dashi da nayi na hakura domin bana son abinda zai canza duka abubuwan da muka shirya a wancan lokacin amma da labarin ta canza tun a wurin zaben dan takara.

Da ga nan ne na mika sunan Osinbajo ga Buhari wanda dama can na taba mika masa a 2011.

Tinubu ya fadi hakanne a wata littafi da Shugaban kwamitin Editocin gidan Jaridar ThisDay Olusegun Adeniyi ya rubuta.

Bukola Saraki ya ce bayan haka bai taba yin dana sani ba akan wannan shawara na Tinubu da yaki amincewa dashi ba.

Ya ce yayi haknne domin kasa Najeriya da mutanen cikinta.

Share.

game da Author