Direbobin tankan mai zasu fara yajin aiki daga gobe Litini a fadin kasar nan.
Idan har direbobin suka shiga yajin aikin za a samu matsalar karancin mai a gidajen mai dake fadin kasarnan.
Direbobin sunce zasu shiga yajin aikin ne saboda kin cika musu alkawuran da gwamnati ta dauka musu wanda ya hada da gyara manyan titunan kasa Najeriya, karancin albashi da rashin samar musu da tsaro.
Kungiyar direbobin sun dade suna kira da a kara musu albashi amma kungiyar NARTO sun yi burus da maganar. Sannan kuma ga matsi da suke fama dashi daga wajen jami’an tsaro.
A haka ma da ake ciki an fara samun dogayen layukan mai a gidajen mai dake wasu jihohin kasarnan.