Dan bautar Kasa Ochai, ya rasu ne a jihar Sokoto bayan ya kammala buga wasar Tamola

1

Shugaban hukumar kula da masu bautar kasa na jihar Sokoto Musa Abubakar ya sanar da rasuwan wani dan bautar Kansa, Anthony Ochai a jihar.

Ya fadi hakan ne a taron yaye ‘yan bautar kasa da aka yi a jihar ranar Juma’a.

Abubakar yace mamacin kafin ya rasu ya yi aikin bautar kasan sa ne a makarantar sakandaren Tsamaye da ke karamar hukumar Sabon-Birni a jihar.

Ya ce mamacin ya rasu ne a dalilin bugawar da zuciyar sa tayi a daidai yana hutawa da yake hutawa bayan ya gama buga wasan kwallon kafa.

Bayan an mika gawar mamacin ga likitoci, sun tabbatar wa hukumar cewa zuciyarsa ta buga ne bayan wasan kwallon kafa.

Abubakar yace marigayi Ochai ya zo aikin bautar kasar ne daga kauyen Ugbokolo dake karamar hukumar Ukopo jihar Benue.

An bizine Ochai jiya juma’a.

Share.

game da Author