Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da dalilan da ya sa take tsare da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido a Kano.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Samba Sokoto ya ce rundunar na tsare da Sule ne saboda wasu kalamai da yayi na ingiza mutane da suyi wa gwamnatin jihar bore a lokacin zaben kananan hukumomi da za’a yi a watan Yuli a jihar.
Sokoto ya ce hakan ya saba wa sashe na 114 na dokar jihar.
Ana nan ana ci gaba da bincike akan wadannan maganganun da Sule yayi kuma rundunar ‘yan sandan ta ce zata sanar da duniya abin da suka gano.
Mataimakin sufritandan ‘yan sanda mai kula da bincike ya ce ‘yan sandan sun tasa keyar Sule ne bayan kukan da gwamnatin jihar ta kawo gabanta cewa gwamnan ya umurci magoya bayansa da su ta da hankalin jama’a a zaben kananan hukumomi da za’ a yi a jihar nan bada dadewa ba.
Sule ya ce ” Kafin wannan zabe sai na tabbatar kowani daya daga cikinku ya yi mini rantsuwa da rayuwansa akan wannan abu da muka sa a gaba.
” Ko ma menene ya faru ba zan saurari kukan ku ba. Abin da nake so kawai Inji shine an nemeni da inzo in bada belin kowani dayanku don ko kun fasa ma wani kai ko kuma kun yi ma wani jina-jina domin wannan gwamnatin mahaukata ce.
Har a zuwa 10:30 na daren lahadi Sule na tsare a ofishin ‘yan sandan.