Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ba a yawan ganin gilmawar sa ya na kazar-kazar bakin aiki, inda ya ce wannan ba wani abin nuna damuwa ba ne.
Da yake magana ta bakin Babban Mai Taimaka Masa ta fannin yada labarai da hulda da jama’a, Malam Garba Shehu, Buhari ya fada a yau Alhamis cewa rashin zuwan sa Taron Majalisar Zartaswa jiya Laraba, wani uziri ne ya taso dab da fara taron, shi ya sa ba a gan shi ba.
Ya kara da cewa idan za a iya tunawa ko lokacin da ya dawo daga jiyyar kwanaki hamsin a Londan, da kansa ya bayyana wa jama’a cewa zai dan ja baya daga gudanar da wasu ayyuka inda zai wakilta mataimakin sa, kafin ya wartsake garau.
Kowa ya san rashin lafiya, warwarewa garau kuma da sannu a hankali ne, amma wannan ba wani abin tayar da jijiyar wuya ko jimami ba ne.
“Shugaba Buhari na samun dukkan bayanan ayyukan da ke wakana a cikin gwamnati, kuma a ko da yaushe ya na ganawa da mataimakin sa, Yemi Osinbajo. Sannan kuma gidan sa ma da ya ke zaune, akwai ofis wadatacce da ya ke gudanar da sha’anin mulki.